Manyan jagororin kungiyar Hamas sun ce maganganun da shugaban kasar Amurka Donald Trump, keyi akan korar Falasdinawa daga Gaza, zai iya lalata yarjejeniyar tsagaita wutar yakin da aka cimma.
:::NDLEA ta kama Maza da Mata su 80 masu shan kayan maye a bikin Birthday a jihar Kano
Trump, dai yayi barazanar yin fatali da duk wata yarjejeniyar zaman lafiya ko tsagaita wuta in har Hamas ta gaza sakin yan kasar Isra’ilan da take tsare dasu.
Sai dai Sami Abu Zuhri, wanda daya ne daga cikin masu magana da yawun Hamas yace mutunta yarjejeniyar da akayi shine kadai zai sanya a saki wadanda kungiyar take tsare dasu.
A jiya Litinin, Hamas ta yi barazanar jan lokaci akan sakin sauran Æ´an Isra’ila da take riÆ™e da su akan zargin Isra’ila da rashin mutunta Æ™a’idojin yarjejeniyar yadda ya dace.
Hujjojin da Hamas ta bayar sun haÉ—a da cewa Isra’ila na yin cikas ga shigar kayan agaji zuwa Gaza da kuma sakin FalasÉ—inawan da ke hannunta, amma Isra’ila ta yi watsi da zargin tare da kara yawan jami’anta a yankin Gaza, bayan cewa yarjejeniyar ta kunshi janye dakarun Isra’ila daga yankin.