Gwamnatin tarayya ta ninka kudin rijistar kafa jami’o’i masu zaman kansu da kaso 400 cikin dari

0
37

Gwamnatin tarayya ta ninka kudin rijistar kafa jami’o’i masu zaman kansu da kaso 400 cikin dari.

Kafin yanzu dai ana biyan Naira miliyan 5 don yin rijistar bude jami’a mai zaman kanta a Najeriya, wanda yanzu ya koma Naira 25.

:::

Hukumar dake kula da jami’o’i ta kasa NUC ce ta sanar da hakan ga manema labarai.

Sanarwar tace ministan ilimi Tunji Alausa, ne ya bayar da umarnin yin karin kudin rijistar, bisa cewa hakan zai kara inganta harkokin jami’o’i masu zaman kansu sake Najeriya.

Bayan haka gwamnatin tarayya ta kare daukar matakin karin kudin da cewa za’a yi amfani dasu ne wajen kula da ayyukan jami’o’in da kuma sahale musu yin aiki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here