CBN ya kara harajin da ake Cajar Mutane Bayan cire Kudi a Na’urar ATM

0
62

Babban bankin kasa CBN, ya sanar da sake bibiyar kudin da yake cajar abokan huldar bankunan kasuwanci bayan sun dauki kudi daga na’urar cirar kudi ta tafi da gidanka ATM.

Mai rikon mukamin daraktan tsare-tsaren harkokin kudi da ka’idoji na bankin John Onojah, ne ya sanar da hakan inda yace matakin zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Maris din shekarar da uke ciki.

:::Gwamnatin Jigawa zata dauki jami’an tsaro 9,970

Yace karin harajin zai saukakawa bankuna tsadar tafiyar da ayyukan su da kuma inganta yanayin harkokin bankunan.

Idan za’a iya tunawa a shekarar 2019 ne babban bankin ya rage harajin cire kudi daga ATM daga naira 65 zuwa 35.

CBN yace za’a caji naira 100, da kuma karin naira 450, akan duk naira dubu 20, da aka cire a ATM din bankin da ba a nan mutum yake da asusu ba.

Amma sanarwar tace masu daukar kudi daga ATM din bankunan da suka bude asusu zasu cigaba da yin ma’amala ba tare da cajar komai ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here