Jami’ar Tafawa Balewa (ATBU) ta bawa daliban ta damar yin amfani da Gas din girki

0
47

Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa dake jihar Bauchi (ATBU) ta bawa daliban ta damar yin girki da Gas, bayan ta hana yin amfani dashi a baya.

Mahukuntan jami’ar sunce daliban zasu iya yin amfani da tukunyar Gas din girki da bata wuce mai nauyin kilogram 3 ba, sabanin yadda aka haramta yin amfani da Gas baki daya ga dalibai saboda tsoron gobara.

Shugaban sashin kula da al’amuran dalibai na ATBU, Farfesa Sa’id Umar, ne ya sanar da hakan a ranar lahadi lokacin da yake yin jawabi a wajen wayar da kan sabbin dalibai da jami’ar ta dauka, inda ya tabbatar da cewa daliban da suka kama wajen zama a jami’ar (hostels) a yanzu suna da damar yin amfani da Gas.

Umar, yace an bayar da wannan dama bayan sake yin Nazari akan dokokin jami’ar, yana mai cewa duk wani dalibin da aka samu yana yin girki da tukunyar Gas data wuce girman 3kg, za’a hukunta shi.

A nasa jawabin shugaban hukumar kashe gobara ta jihar Bauchi, Umar Lawal, yace kaso 90, na tashin gobara ana samun sa daga sakaci da rashin kiyaye ka’ida.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here