Gwamnatin tarayya ta fara karbar sabon haraji akan kayan da aka shigo dasu Nigeria

0
67
Tinubu
Tinubu

Masu sarrafa kayayyaki sun kalubalanci harajin kaso 4 cikin dari akan kayan da aka shigo dasu Nigeria daga kasashen waje.

Wasu daga cikin masu kamfanonin sarrafa kayayyaki sun nuna kin amincewa da sabon harajin.

A makon daya gabata ne dai hukumar hana fasa kwauri ta kasa Customs, ta sanar da sanya sabon harajin, wanda masu ruwa da tsaki da masana harkokin tattalin arziki ke kalubalanta.

Masana harkokin tattalin arziki sun shaida cewa karin harajin ka’iya sake jefa yan Nigeria a yanayin matsalolin kudi.Sannan masana sunce karin harajin zai karya alkawarin gwamnatin tarayya na saukakawa mutane tashin farashin kayayyakin masarufi a wannan shekara ta 2025.

A litinin data gabata ne aka kara harajin shigo da kayayyakin daga kaso 1, zuwa kaso 4, cikin dari.

Wani binciken da aka gudanar a tashar shigo da kayayyaki ta ruwa ta Tin-Can dake jihar Lagos, ya nuna cewa an fara karbar sabon harajin a ranar Talata data gabata, wanda aka bayyana hakan a matsayin wani matakin da zai gurgunta kasuwanci daga tashoshin shigo da kaya ta ruwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here