Atiku Abubakar ya gana da Olusegun Obasanjo a Abeokuta

0
50

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya ziyarci tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, inda suka yi ganawar sirri a dakin karatu na (OOPL) dake Abeokuta a jihar Ogun.

Babban na kusa da Obasanjo, Otunba Oyewale Fasawe, ne ya tarbi tawagar Atiku, a dakin karatun da misalin karfe 12:36, na rana a yau litinin.

Wasu daga cikin mutanen da suke cikin tawagar Atiku Abubakar, sun hadar da tsohon gwamnan jihar Cross River, Liyel Imoke, Aminu Tambuwal, da Sanata Abdul Ningi daga jihar Bauchi.

Kawo yanzu ba’a bayyana abubuwan da ziyarar ta kunsa ba, sai dai ana kyautata zaton bata rasa nasaba da yanayin siyasar Najeriya, a kakar zabe ta shekarar 2027.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here