Ɗan Bijilanti ya kashe budurwar sa da duka bayan yi mata ciki

0
54

Wani ɗan Bijilanti ya kashe budurwar sa da duka, bayan taki amincewa a zubar da cikin da yayi mata.

Wannan lamari ya faru a unguwar Okpara Olomo ta karamar hukumar Ughelli ta kudu dake jihar Delta, inda ake zargin Olu da kisan Ejiro.

Rahotanni sun tabbatar da cewa kin amincewa da Ejiro, tayi a zubar da cikin da Olu, yayi mata ne yasa shi yi mata dukan da sai da ta fita daga hayyacin ta daga bisani ta rasu.

Ance a ranar 4 ga watan Fabrairu ne masoyin Ejiro ya kira ta zuwa gidan sa da yammaci wanda daga nan aka fara samun sabanin da ya kai aka yi kisan kai.

Bayan ya kashe ta ne ya dauki gawar ta inda ya jefar akan hanya, wanda aka samu gawar a safiyar 5 ga watan Fabrairu.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Delta, SP Bright Edafe, yace zai yi karin haske akan lamarin bayan gudanar da bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here