Ɗan sanda ya kashe kansa a jihar Niger

0
44

Ɗan sanda mai mukamin ASP ya kashe kansa a jihar Niger.

ASP Shafi’u Bawa, ya aikata kisan kan nasa da yammacin ranar Asabar.

An gano gawar sa rataye a jikin saman ɗakin sa bayan da mahaifinsa, Mallam Usman Bawa, ya fara fahimtar abin da ya faru sannan ya kai rahoto zuwa ofishin ‘yan sanda na Kontagora, bayan ya samu dan nasa ya rataye kansa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

Yace tuni aka gudanar da bincike tare da mika gawar ga yan uwan sa, wanda tuni aka binne shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here