Rahotanni sun tabbatar da cewa daya daga cikin sansanin ‘yan ta’adda mai karfi na tungan fulani dake Jihar Zamfara ya dawo karkashin ikon sojojin Najeriya.
Zuwa yanzu sojojin sun kafa tutar Nigeria akan tsaunin sansanin, da hakan yake tabbatar da kwace shi daga hannun bata garin.
Sannan an bayar da labarin hallaka yan ‘yan ta’adda fiye da 40, yayin kwace wajen.
A yan kwanakin nan dai rundunar sojin kasa ta sanar da karfafa yakar ayyukan ta’addanci, inda a jiya asabar ta sanar da kashe manyan kwamandojin dan ta’adda Bello Turji, a jihar Zamfara.