Na rantse da Allah Aisha Binani ce ta lashe zaben gwamnan jihar Adamawa—Hudu Ari

0
63

Tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa reshen jahar Adamawa da aka kora daga aiki Hudu Ari, yace ba’a yi masa adalci ba, wajen yanke hukuncin korar sa daga aiki.

Yace an yake hukuncin ne ba tare da an saurari hujjojin da ya dogara dasu ba.

Sannan yayi rantsuwa da Allah akan cewa Aisha Binani, ta jam’iyyar APC ce ta lashe zaben gwamnan jihar Adamawa, a shekarar 2023, sabanin Ahmadu Fintiri na PDP da aka sanar.

Idan za’a iya tunawa Hudu Ari, ya bayyana sakamakon zaben jihar Adamawa, a shekarar data gabata tun kafin a kai ga kammala tattara sakamakon zaben, duk da cewa ba shine mai alhakin bayyana sakamakon ba.

Wannan abu shine dalilin korar sa daga aiki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here