Wuta ta kone motoci da kayan abinci a yankin Sabon Wuse dake karamar hukumar Tafa a jihar Nijer, sakamakon fashewar motar dakon Gas.
Daily trust, ta rawaito cewa fashewar ta faru lokacin da motar dakon Gas ke sauke Gas din ta dauko, a wani wajen siyar da Gas din dake wannan unguwa.
Majiyar Daily trust, daga bakin wani mazaunin inda abin ya faru mai suna Abdul Sabon-Wusa, tace Wutar ta tashi da misalin karfe 11 na daren jiya asabar, kuma ta dauki awanni tana ci kafin isowar jami’an kashe gobara.
Yace karar fashewar tankar dakon man ta sanya firgici a zukatan al’ummar yankin da lamarin ya faru, har ma wasu suka yi gudun tsira da rayuwar su, amma yace ba’a samu asarar rai ba.