Matasa sun jefi motar Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II

0
144

Wasu matasa biyu sun jefi motar Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sunusi II, a unguwar Kabara, lokacin da zai kai ziyara unguwar Kofar Mata, a ranar asabar.

Rahotanni sun bayyana cewa masu tsaron lafiyar Sarkin sun yi harbi a iska wanda ya sanya tsagerun matasan guduwa.

Kawo yanzu dai ba’a ji masarautar Kano ta ce komai ba, dangane da batun jifan, kamar yadda majiyar Premier Radio ta bayyana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here