Gwamnan jihar Abdullahi Sule, yayi zargin cewa jami’an hukumar kula da Malamai ta Jihar sune ke da alhakin hakan, wajen karɓar kudi daga mutanen da basu cancanta ba don basu aikin koyarwa.
Gwamnan ya kuma yi barazanar daukar matakin shari’a akan jami’an, inda yace zai mika su ga jami’an tsaro don bayyana gaskiyar abinda yasa aka dauki mutanen da basu da kwarewa aka basu koyar da dalibai.
Jihohin arewa dai na fama da karancin ingantattun malaman boko, wanda idan za’a iya tunawa ko a shekarun baya sai da tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i, ya kori tarin malamai masu yawa da aka tabbatar basu da kwarewar koyarwa.
Ko a yan kwanakin da suka shude tsohon gwamnan jihar Nijer Babangida Aliyu, shima yace kaso 50 na malaman arewa basu cancanci koyarwa ba, yana mai cewa wannan ne dalilin da yasa ba’a samun hazikan dalibai daga arewa.