Shugaban karamar hukumar Bade dake jihar Yobe, Ibrahim Babagana, ya bayyana cewa ciwon ƙoda ya kashe mutane 6, daga cikin yan uwansa.
Shugaban karamar hukumar, ya sanar da hakan a lokacin da wata tawagar masu bincike akan yawaitar ciwon ƙoda a jihar ta kai masa ziyara.
Ya kuma yabawa gwamnan jihar Mai Mala Buni, bisa yadda ya nuna damuwa dangane da matsalar karuwar masu fama da cutar, da kuma daukar matakin binciken dalilin yawaitar cutar a Yobe.
Jihar Yobe dai na fama da matsalolin yawaitar masu kamuwa da ciwon ƙoda, wanda hakan ke kashe mutane babu adadi.