An gano jirgin fasinjojin daya bace da mutane 10 a Amurka

0
63

Mahukuntan kasar Amurka sun tabbatar da gano tarkacen wani karamin jirgin fasinjoji 10, da aka nema aka rasa a jihar Alaska, a ranar juma’ar data gabata.

Sakataren harkokin sufuri na Amurka, Sean Duffy, ya roki al’umma su yiwa mutane 10 dake cikin jirgin addu’a, sakamakon cewa sun rasa rayukan su, duk da cewa zuwa yanzu mutane 3 na cikin jirgin aka tabbatar sun mutu.

Idan za’a iya tunawa a ranar juma’ar data gabata ne mahukuntan gwmanatin Amurka suka ce sun dukufa wajen neman wani karamin jirgin daya bata mai dauke da mutane 10, a jihar Alaska.

Masu kula da gaɓar teku a yankin Alaska sun ce jirjin samfurin Cessna Caravan ya yi nisan kilomita 19 daga Unalakleet zuwa Nome a lokacin da aka rasa shi.

A cewar sashen kula da alumma na Alaska, mutum 10 ne ke cikin jirgin, da suka haɗa da fasinjoji 9 da matuƙin jirgi ɗaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here