Ɗan shekara 10 ya yiwa yar shekara 3 fyade

0
37

Jami’an yan sanda sun kama karamin yaro ɗan shekaru 10 da ya yiwa yar shekara 3 fyade.

Jami’an yan sandan jihar Akwa Ibom, ne suka tsare yaron, wanda ya amsa laifin da ake zargin sa da aikatawa.

Kakakin rundunar yan sandan Timfon John, ce ta sanar da hakan a jiya Asabar.

A gobe litinin 10 ga watan Fabrairu za’a gurfanar da yaron a gaban shari’a, wanda shine yakai kansa da kansa zuwa ofishin yan sandan.

Rundunar ta nemi al’umma su kwantar da hankalin su tare da cewa za’a yi adalci akan shari’ar da za’a yiwa karamin yaron.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here