Yan bindigar da suka yi garkuwa da tsohon shugaban hukumar masu hidimar kasa NYSC Janar Maharazu Tsiga, mai ritaya sun nemi a biya kudin fansar sa har Naira 250.
Rahotanni sun tabbatar da cewa maharan da sace Tsiga, tare da wasu mutane 9 a daren ranar Larabar wannan mako a jihar Katsina sun ce sai an biya waÉ—ancan makudan kudade zai shaki iskar yanci.
Wasu yan bindiga fiye da 100, ne dai suka sace su a kauyen Tsiga dake karamar hukumar Bakori, lokacin da suke tsaka da bacci.
Wata Majiya data nemi sakaya sunan ta daga iyalan mutumin, ta bayyanawa jaridar Daily trust, cewa masu garkuwar sun tuntube su akan bukatar biyan kudin fansa.
Kawo yanzu rundunar yan sandan jihar Katsina ba tace komai ba
dangane da batun biyan kudin fansar, sakamakon ba’a samu damar jin ta bakin su ba.