Rundunar Sojin Nigeria ta sanar da kashe manyan kwamandojin Bello Turji

0
92

Hafsan hafsoshin tsaron Nigeria Christopher Musa, yace sun kashe manyan kwamandojin dake taimakawa fitaccen dan ta’adda Bello Turji.

Musa, ya bayyana hakan a birnin tarayya Abuja ranar Juma’a.

A kwanakin baya ne dai aka rika yada jita jitar cewa sojin Nigeria sun kashe fitaccen dan ta’adda Bello Turji, yayin wani hari da suka kaiwa maboyar sa a Zamfara, duk da cewa daga bisani rundunar ta sanar da cewa kashe ko kama Turji ba.

Amman Sojin sunce suna gab da kawo karshen Turji, wanda ya addabi Zamfara, Katsina da kewaye.

Turji dai yayi kaurin suna wajen yin garkuwa da mutane, sace dabbobi da kisan al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here