Gwamnatin Nigeria ta kwace lambar zama ɗan ƙasa NIN 6000 da aka yiwa yan jamhuriyar Nijar

0
45

Gwamnatin tarayya ta bankado mutane dubu shida yan asalin jamhuriyar Nijar, da aka yiwa lambar shaidar zama ɗan ƙasa ta Nigeria NIN.

Gwamnatin tarayyar ta sanar da haka lokacin da shugaban Kasa Tinubu, ya bayar da umarnin yin gyara a kundin tattara bayanan yan Nigeria da aka yiwa lambar zama ɗan ƙasa.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da samun adadin yan Nijar din da aka yiwa lambar, a ranar 4 ga Fabrairu, lokacin zaman majalisar zartarwa ta tarayya.

Yace zuwa yanzu an goge bayanan mutanen daga kundin tattara bayanan yan Nigeria dake hukumar kula da yiwa yan Nigeria shaidar zama ɗan ƙasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here