Gwamnan Kano ya naɗa sabon sakataren gwamnatin jihar

0
133

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya nada Umar Farouk Ibrahim, a matsayin sabon sakataren gwamnatin jihar.

Kakakin gwamnan Kano Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa daya fitar a daren asabar.

Sanarwar tace nadin zai fara aiki daga ranar 10, ga watan Fabrairu da muke ciki.

Dawakin Tofa, yace an zabi sabon sakataren gwamnatin bisa duba cancanta da karewa, tare da fatan inganta cigaban ayyukan gwamnati.

Haka zalika sanarwar ta kara da cewa Umar Farouk, yana da kwarewar aiki data wuce ta shekari 30, wanda yayi aikin gwamnati a tsakanin shekarun 1987 zuwa 2023, sannan ya taka rawa a wajen samar da cigaban sha’anin gudanarwa a gwamnatin jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here