Babbar Kotun tarayya ta saka lokacin cigaba da yin shari’ar jagoran kungiyar (IPOB) Nnamdi Kanu

0
39

Babbar kotun tarayya dake Abuja zata cigaba da tuhumar Nnamdi Kanu, a ranar 10 ga watan Fabrairu 2025.

Kotun ta bukaci a gabatar mata da Kanu, don cigaba da yi masa shari’ar da gwamnatin tarayya ta shigar dashi kara kan zargin cin amanar kasa.

Nnamdi Kanu, dai shine jagoran kungiyar dake rajin kafa kasar Biapra(IPOB) don ballewa daga Nigeria.

Mai shari’a Binta Nyako, ce zata cigaba da sauraron shari’ar duk da cewa a baya ta nesanta kanta daga cigaba da yin shari’ar Nnamdi Kanu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here