Rundunar yan sandan Nigeria ta tabbatar da sace wasu mutane 10, lokacin da suke yin Sallar Asubahi a garin Bushe, na yankin sabon Birni dake jihar Sokoto.Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar ne ya bayyana hakan a jiya Juma’a lokacin da yake zantawa da manema labarai dangane da sace masallatan, yana mai cewa yan bindiga ne suka shiga garin lokacin da ake yin Sallar Asubahi tare da sace mutanen da suka fito Masallaci don gudanar da ibada.
Yace, a wannan yanayi na zulumin sace masallatan yan sandan jihar tare da sauran jami’an tsaro sun dukufa wajen kubutar da mutanen da aka sace.
Al’ummar garin sun ce Limamin Masallacin garin na Bushe na daga cikin wadanda maharan suka yi garkuwa da su.