Mahukuntan gwmanatin Amurka sun dukufa wajen neman wani karamin jirgin daya bata mai dauke da mutane 10, a jihar Alaska.
Masu kula da gaɓar teku a yankin Alaska sun ce jirjin samfurin Cessna Caravan ya yi nisan kilomita 19 daga Unalakleet zuwa Nome a lokacin da aka rasa shi.
Cikin wata sanarwa da hukumomin jihar suka fitar, sun ce ma’aikatan ceto na cigaba da ƙoƙarin gano wurin da yake.
A cewar sashen kula da alumma na Alaska, mutum 10 ne ke cikin jirgin, da suka haɗa da fasinjoji 9 da matuƙin jirgi ɗaya, sai dai har yanzu babu cikakkun bayanai akan mutanen.