NNPCL ya karyata labarin tashin gobara a matatar fetur ta Warri

0
74

Kamfanin mai na kasa NNPCL, ya yi karin haske akan cewa babu kamshin gaskiya a zancen fashewar wasu abubuwa a matatar man fetur ta Warri, dake jihar Delta.

Mai magana da yawun kamfanin Olufemi Soneye, ne ya bayyana hakan a yau juma’a cikin wata sanarwa daya fitar yana mai cewa babu wata wutar data tashi a matatar kuma wannan zance ba gaskiya bane.

Sai dai Soneye, yace a ranar 25 ga watan Junairu an dakatar da ayyuka a wani sashin matatar saboda gudanar da wasu gyare-gyaren kayan aikin tace fetur don inganta yanayin matatar.

Yace wannan gyara zai inganta tace dangogin man fetur musamman Gas da kalanzir, tare da cewa hakan bai hana gudanar da ayyuka a matatar Warri ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here