NAFDAC na son yanke hukuncin kisa akan masu cinikin jabun magunguna

0
40

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa, NAFDAC ta nemi a rika yanke hukuncin kisa ga masu haɗawa da shigar da jabun magunguna cikin Nigeria.

A cewar shugabar hukumar Mojisola Adeyeye, tsauraran matakai ne kawai za su hana aikata hakan musamman idan lamarin yana kai wa ga mutuwar yara.

Ko a jiya majalisar wakilai ta buƙaci babban mai shari’a na tarayya da ya gabatar da tsauraran takunkumai da suka hada da ɗaurin rai da rai ga masu haɗawa da masu shigo da magungunan jabu cikin ƙasar.

Bayan muhawara kan ƙudurin wanda ya samu goyon bayan ƴan majalisar, majalisar ta buƙaci babban lauyan gwamnatin tarayya da ya gabatar da gyara ga dokokin da ake da su da nufin zartar da hukunci mai tsauri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here