Mayakan Lakurawa sun kai sabon hari jihar  Kebbi

0
96

Wani hari da mayakan Lakurawa suka kai yankin Gulma, a karamar hukumar Argungu dake jihar Kebbi, yayi sanadiyyar mutuwar mutum daya da jikkata wasu 6, da a yanzu suke kwance a asibiti.

Rahotanni sun bayyana cewa mayakan sun kai harin da tsakar daren ranar Alhamis kusan karfe 11, lokacin da mutanen ke tsaka da bacci.

Tuni dai harin ya kashe mutum 1, sannan mutane 6, sun samu raunin harbin bindiga, da ake cigaba da basu kulawa a Cibiyar kula da lafiya ta gwamnatin tarayya dake birnin Kebbi.

Kakakin rundunar yan sandan jihar CSP Nafi’u Abubakar, ya tabbatar da kai harin, sannan yace tuni aka tura yan sandan tafi da gidan ka zuwa yankin da aka kai harin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here