ICPC ta kama mataimakin kwamandan Civil Defence akan zargin almundahana 

0
57

Hukumar yaki da cin hanci da cin hanci rashawa da dangogin su ta kasa ICPC, ta kama mataimakin kwamandan rundunar tsaron al’umma ta Civil Defence, na jihar Kogi Adam Yusuf, akan zargin almundahana tare da kama tsohon hafsan sojin ruwa na kasa Usman Jibrin, akan zargin karkatar da Naira biliyan 3.Usman Jibrin, ya kasance tsohon hafsan sojin ruwa na Nigeria tsakanin shekarar 2014 zuwa 2015.

Daraktan wayar da kan al’umma na hukumar ICPC, Demola Bakare, ne ya sanar da hakan, yana mai cewa nan gaba kadan za’a gurfanar da mutanen a gaban kotu don fuskantar hukunci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here