Gwmanatin tarayya ta karyata labarin rushe tsarin karama da babbar sakandire

0
185

Ministan ilimi na tarayyar Nigeria Dr. Tunji Alausa, ya karyata labarin rushe tsarin karama da babbar sakandire wato JSS da SSS don sauya shi da tsarin Ilimin bai daya na shekaru 12.

Daraktar yada labarai da hulda da jama’a ta ma’aikatar Folasade Boriowo, ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa data fitar a yau juma’a a birnin tarayya Abuja.

Boriowo, tace ministan Ilimin ya tabbatar da cewa babu maganar rushe tsarin karama da babbar sakandire don sauya shi da tsarin Ilimin bai daya na shekaru 12.

 Sai dai sanarwar tace minista Alausa, ya gabatar da bukatar sauya tsarin karatun Nigeria, wanda a yanzu haka ba’a kai ga yanke shawara akan bukatar daya fitar ba a lokacin wani taron daya shafi harkokin ilimi a ranar 6 ga watan Fabrairu.

Yace bukatar daya gabatar ta nemi a canja tsarin yin shekara 6 a Firamare 3 a karamar sakandire da shekaru 3 a babbar sakandire, tare da komawa tsarin Ilimin bai daya dole na shekara 12.

Alausa, ya kara da cewa manufar gabatar da bukatar shine a kawo karshen banbancin dake tsakanin rubuta jarrabawar JSS da SSS.

Yace sai a watan Oktoba, za’a yanke shawara akan yin amfani da tsarin ko kyale shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here