Yan bindiga sun sace tsohon shugaban hukumar NYSC da wasu mutane a Katsina

0
58

Wasu yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon shugaban hukumar masu hidimtawa kasa NYSC, Manjo Janar Mahraz Tsiga, tare da wasu mutanen kauyenTsiga a karamar hukumar Kankara, ta jihar Katsina.

:::Ghana ta rage kudin aikin hajjin shekarar 2025 zuwa Cedi 62000

Rahotanni sun bayyana cewa an sace mutanen da tsakar daren Laraba.

Wata majiya ta bayyanawa Prime time, cewa tabbas tsohon shugaban hukumar ta NYSC, na daga cikin wadanda aka sace a kauyen na Tsiga.

Kwamishinan tsaro da al’amuran cikin gida na jihar, Katsina Dakta Nasiru Mu’azu ya tabbatar da cewa an sace Manjo Janar Tsiga a garin Tsiga da ke yankin Æ™aramar hukumar Kankara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here