Shugaban kasa Tinubu ya kori shugabar jami’ar Abuja

0
51

Shugaban kasa Tinubu, ya kori Farfesa Aisha Sani Maikudi, daga shugabancin jami’ar birnin tarayya Abuja, da aka sauyawa suna zuwa jami’ar Yakubu Gowon.

Mai taimakawa shugaban kasar a fannin yada labarai Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan, cikin wata sanarwa daya fitar a yau alhamis, yana mai cewa hakan ya samo asali daga wasu canje canjen mukamai da shugaban yayi a wasu jami’o’in tarayya.

Sanarwar tace Tinubu, ya rushe daukacin shugabancin jami’ar Yakubu Gowon, tare da bayyana shugabancin rikon kwarya.

Tuni aka ayyana sunan Farfesa Lar Patricia, a matsayin shugabar jami’ar Yakubu Gowon, ta riko da zata rike mukamin na tsawon watanni 6.

A wani cigaban shugaban kasar ya cire Farfesa Polycarp Emeka Chigbu, daga mukamin sa na na rikon shugaban jami’ar Nsukka, kafin karewar wa’adin sa a ranar 14 ga watan Fabrairu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here