Rashin lantarki ya tsananta a Kaduna sakamakon yajin aikin ma’aikatan (KAEDCO)

0
31

Al’ummar jihar Kaduna sun shiga wuni na uku ba tare da ganin hasken lantarki ba, biyo bayan yajin aikin da ma’aikatan kamfanin lantarki na jihar (KAEDCO) , ke gudanarwa.

:::An samu gawar dan majalisar da aka sace a jihar Anambra

Daukewar lantarkin ta kuma haifar tsananin rashin ruwan sha a unguwannin kwaryar birnin Kaduna, irin su Unguwar Romi, Sabo, Unguwar Maijero, da sauran su, kuma hakan ya sanya manya da kananun yara daukar kayan neman ruwa don samo ruwan sha daga rijiyoyin burtsatse da basa yin amfani da lantarki, ko kuma wadanda ake amfani da hasken rana.

Sai dai duk da haka masu ruwa da tsaki a fannin lantarkin jihar Kaduna, sun cigaba da bawa mutane hakurin cewa nan bada jimawa ba, zasu shawo kan yajin aikin da kuma dawo da wuta kamar yadda aka saba yin amfani da ita a baya.

Jami’in hulda da jama’a na kamfanin (KAEDCO) Abdullahi Abdullazeez, ya fitar da wata sanarwa a ranar Larabar data gabata, yana mai cewa suna sane da halin kuncin da rashin lantarki ya jefa al’umma, musamman iyalai da masu sana’o’in da suka dogara da lantarki.

Ma’aikatan kamfanin KAEDCO, dai sun shiga yajin aikin bisa zargin cewa kamfanin yana yin shirin korar mutame 900, daga cikin ma’aikatan, duk da cewa KAEDCO, yayi karin hasken cewa mutane 450, ya shirya kora ba 900, ba.

Kawo wannan lokaci dai masu sana’o’in da suke yin amfani da lantarki a Kaduna, sun shiga tsaka mai wuya saboba koma bayan harkokin su na yau da kullum yayin da wasu suka fara yin asara, musamman masu sana’ar ajiye danyen nama, kifi da sauran kayan masarufi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here