Dan sanda ya harbe kansa da bindiga

0
88

Jami’in rundunar yan sandan kasa dake aiki a jihar Nasarawa yayi ajalin kansa da kansa ta hanyar bindige kansa.

Dan sandan mai suna Dogara Akolo-Moses, ya kasance mai yin aiki a ofishin yan sanda na yankin Mada dake karamar hukumar Nasarawa Eggon, a lokacin daya kashe kan nasa.

:::Yan bindiga sun sace tsohon shugaban hukumar NYSC da wasu mutane a Katsina

Wadanda lamarin ya faru a gaban idanun su sun shaida cewa dan sanda ya kashe kansa ta hanyar shiga daki ya bankawa kansa bindiga, da haka yayi sanadiyyar rasuwar sa har lahira.

  • Karar bindigar ce ta janyo hankalin sauran mutane inda aka same shi cikin jini tare da bindigar sa a gefe, wanda har yanzu an gaza sanin dalilin sa na aikita wannan danyen aiki.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Nasarawa, Ramhan Nansel, ya tabbatar da faruwar kisan, yana mai cewa suna kan gudanar bincike akan hakan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here