An gano gawar dan majalisar dokokin jihar Anambra mai suna Justice Azuka, da aka sace tun lokacin gabatowar bukukuwan kirsimetin shekarar 2024.
An gano gawar tasa a yau Alhamis da aka jefar a karkashin wata babbar gadar wucewa dake jihar ta Anambra.
:::Dan sanda ya harbe kansa da bindiga
Yan bindiga ne suka sace dan majalisar yayin da yake tafiya tare da iyalansa a yankin Ugwunakpakpa, dake Onisha.
Jami’an tsaron dake binciken sace dan majalisar sun kama wasu mutanen da ake zargin suna da hannu a yin garkuwar, tare da tafiya dasu wani waje da aka samu gawar magoya bayan jam’iyyar LP.
Rundunar yan sandan jihar Anambra, ta tabbatar da kisan Azuka, ta bakin kakakin ta SP Tochuchu Ikenga.
Azuka, shine dan majalisar dokokin jihar Anambra, na 2 da aka kashe cikin shekaru 2.