Shugaban kasa Tinubu, ya tafi kasar Faransa, a ziyarar Ƙashin kansa.
Mai taimakawa shugaban kasar a fannin yada labarai Bayo Onanuga, ne ya sanar da hakan, yana mai cewa bayan Faransa, Tinubu, zai zarce kasar Ethiopia don halartar taron kungiyar hadin kan kasashen Afrika, da zai gudana a tsakanin ranakun 12 zuwa 16 na watan Fabrairu a birnin Addis Ababa.
Yawaitar tafiye-tafiyen Tinubu, zuwa kasashen ketare na haifar da suka daga yan Nigeria, da suke cewa kamata yayi shugaban ya mayar da hankali wajen magance matsalolin da kasar ke ciki.
Amman ministan harkokin waje na kasa Yusuf Tuggar, yace akwai alfanu a tafiye-tafiyen Tinubu, saboda ya samowa kasar zuba jari na sama da dala biliyan 2, daga kasashen waje.