Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero ya ziyarci shugaban kasa Tinubu akan rikicin Rimin Zakara

0
1249

Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero yayi wata ganawa ta sirri da Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu mintuna kadan kafin tashin shugaban zuwa Faransa.

Sakataren Yada Labarai na Sarkin, Abubakar Balarabe Kofar Naisa, ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa daya fitar a yau Laraba.Yace ganawar da Alhaji Aminu Ado Bayero, yayi da shugaban kasar tana da nasaba da iftila’in daya faru ga al’ummar Rimin Zakara dake yankin Karamar Hukumar Ungogo a jihar Kano.

Sanarwar tace Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyanawa shagaban kasar damuwa akan halin da al’ummar yankin suka tsinci kansu a ciki, musamman kisan mutane 4 da jikkata wasu da dama baya ga rushe gida akalla 50.

Shugaban ya tabbatarwa da Alhaji Aminu Ado Bayero cewa za’ayi duk mai yuwuwa domin ganin an warware takaddamar rikicin filin dake tsakanin al’ummar Rimin Zakara da jami’ar Bayero.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here