Majalisar dokokin Kano ta kalubalanci jami’ar Bayero akan rushe garin Rimin Zakara

0
79

Majalisar dokokin jihar Kano ta nuna takaicin ta akan kalaman shugaban jami’ar Bayero, dangane da batun yin rusau a filin jami’ar dake garin Rimin Zakara.

Farfesa Sagir Adamu, ya sanar da cewa hukumar gudanarwar Bayero ba zata saurara ba wajen ganin an rushe duk wani ginin da akayi a filin da jami’ar tace nata ne tsawon shekaru.

Tuni dai majalisar ta bayyana yin ala wadai da kalaman shugaban jami’ar, bayan da daya daga cikin mambobin majalisar ya gabatar da kudirin bukatar neman hana jami’ar Bayero, cigaba da daukar matakin rusau a garin na Rimin Zakara.

Dan majalisar mai wakiltar karamar hukumar Ungogo, Aminu Sa’adu, ne ya bukaci hakan, bayan lamarin daya faru na kisan mutane 4, a lokacin da jami’an gwamnatin Kano suke yin rusau a Unguwar Rimin Zakara, a daren lahadin data gabata.

A yayin wancan rusau dai anyi asarar fiye da gidaje 50, tare da jikkata wasu mutanen sakamakon rikicin daya biyo bayan rusau din a tsakanin al’umma da jami’an tsaro masu bayar da kariya ga masu rushe gidajen.

Jami’ar Bayero, ta Kano dai tace itace ta mallaki wurin da akayi rusau din wanda wasu mutane ke neman danne mata hakkin ta na mallaka.

Sai dai gwmanatin Kano, ta hannun kwamishinan yada labarai da al’amuran cikin gida, Ibrahim Abdullahi Waiya, tace zata binciki abinda ya faru a Rimin Zakara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here