Gwamnatin jihar tace zata dauki matakin hukunta duk wanda aka samu da laifin sare bishiyun dajin Falgore.
Mai bawa Gwamnan jihar shawara akan harkokin Namun daji da Gandun daji, Halliru Sawaba, ne ya sanar da hakan lokacin da ya kai ziyarar ganin yanayin da dajin na Falgore, ke ciki.
Sawaba, yace daukar matakin ya zama wajibi saboda sare bishiyun nada babbar barazana ga cigaban muhalli.
Ya kuma yaba wa ma’aikatan da ke kula da Dajin a bisa namijin Æ™oÆ™arin da suke yi wajen kare Dajin daga dukkan wata barazanar da take tunkarar sa.
A nasa bangaren, babban jami’in dake kula da dajin falgore, Alhaji Isham sani Aliyu, ya bukaci Mashawarcin gwamnan da ya isar da koken su wajen gwamna na bukatar Æ™arin kayan aiki da ma’aikata domin aikin nasu ya ci-gaba da tafiya yadda ya kamata.
Isham ya kuma bayyana muhimmancin tsaftace dajin daga kowacce barna, duba da illar da rashin yin hakan zai haifar.
A karahe Sawaba ya bada tabbacin isar da bukatun su ga gwamnan Kano, don samun nasarar abinda ake bukata.