Gwamnatin kasar Saudiyya ta fito fili ta kalubalanci shirin gwamnatin Amurka karkashin jagorancin Donald Trump, na bayyana son kwace yankin Zirin Gaza, daga wajen Falasdinawa don mayar da shi wajen yawon bude ido.
Cikin manufar Amurka na kwace Zirin Gaza, akwai shirin korar baki dayan Falasdinawan dake rayuwa a yankin, wanda a yanzu haka Isra’ila ke mamayewa.
A cikin martanin Saudiyya, tace ba zata taba gyara alakar diflomasiyya tsakanin ta Isra’ila ba har sai an samarwa Falasdinawa cikakkiyar kasa mai yanci.
Tuni dai ministan harkokin waje na Saudiyya ya sanar da kin amincewa da wannan shiri na Amurka, da tace zata samarwa Falasdinawan da zata kora daga Zirin wani wajen domin cigaba da yin rayuwa.