Shugaban majalisar Dattawa Sanata Godswill Akpabio, ne ya sanar da cewa shugaban kasa Bola Tinubu, ya saka hannun akan kudirin samar da kwalejin kimiyya da fasaha ta tarayya a garin Rano na jihar Kano, da kuma samar da jami’ar kimiyyar lafiya a Tsafe dake jihar Zamfara.
:::Hukumar Kwastam ta kama muggan makamai a Legas
Akpabio, bai sanar da a wacce rana Tinubu, ya saka hannu kan amincewa da kudirorin ba, sai dai hakan yazo kwana guda bayan da shugaban kasar ya saka hannu kan kudirin kafa jami’ar muhalli da kimiyya ta tarayya a jihar Rivers.