Shugaban kasa Tinubu ya saka hannu kan dokar kafa hukumar cigaban arewa ta tsakiya

0
76
Bola Ahmed Tinubu
Bola Ahmed Tinubu

Shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio, ya sanar da cewa Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu, saka hannu akan kudirin samar da hukumar cigaban arewa ta tsakiya.

An dai jima ana son shugaban kasar ya amince a kafa hukumar don samar da ayyukan more rayuwa da inganta al’ummar yankin.

Bayan haka, shugaban majalisar Dattawan ya sanar da cewa shugaban kasa Bola Tinubu, ya saka hannun akan kudirin samar da kwalejin kimiyya da fasaha ta tarayya a garin Rano na jihar Kano, da kuma samar da jami’ar kimiyyar lafiya a Tsafe dake jihar Zamfara.

:::Hukumar Kwastam ta kama muggan makamai a Legas

Akpabio, bai sanar da a wacce rana Tinubu, ya saka hannu kan amincewa da kudirorin ba, sai dai hakan yazo kwana guda bayan da shugaban kasar ya saka hannu kan kudirin kafa jami’ar muhalli da kimiyya ta tarayya a jihar Rivers.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here