Masu arziki ne suke amfanar tallafin wutar lantarkin da muke biya duk wata—Gwamnatin Tinubu

0
49

Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa a kowanne wata tana kashe naira biliyan 200, a matsayin tallafin wutar lantarki.

Gwamnatin tace attajirai ne ke amfanar tallafin da take biya, wanda a cewar ta sune kaso 25, na yawan al’ummar Nigeria, tare da cewa mutanen da ake biyan tallafin sabo da su wato talakawa basa cin moriyar tallafin.

:::A yau ne yan majalisa zasu dawo daga hutu da suka tafi

Mai taimakawa Tinubu a fannin makamashi Olu Verheijen, ce ta sanar da hakan cikin wata sanarwar data fitar a jiya litinin.

Olu Verheijen, ta bayyana haka ne a matsayin mayar da martani ga labaran da aka yada masu nuni da cewa gwamnatin tarayya zata kara farashin lantarki da kaso 2, cikin 3, na abin da ake biya a yanzu, don inganta fannin wutar.

Sai dai a cikin martanin nata bata musanta labarin karin kudin wutar ba, amma tace babu maganar karin da kaso 65, cikin dari.

Tace asalin talakawan da suka cancanci morar tallafin basu cin wata riba daga abinda gwamnatin tarayya ke biya a kowanne wata.

Tace ko kadan ba’a fassara kalaman ta yanda ya kamata ba, inda ta bayyana cewa abinda take nufi shine duk da an kara kudin lantarki na layin Band A, har yanzu kudin da ake tattarawa basa isa a samar da lantarkin har sai gwamnati ta bayar da tallafi.

Kafafen yada labarai dai sun ce Olu, ta ce za’a kara kudin lantarkin da kaso 65, cikin dari, lokacin da ta wakilci Nigeria a wani taron makamashi na Afrika, daya gudana a Tanzania.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here