Malaman jami’ar jihar Kaduna zasu shiga yajin aiki a watan da muke ciki

0
45

Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU, reshen jami’ar jihar Kaduna KASU, ta sanar da shirin ta na tsunduma yajin aikin sai baba ta gani daga ranar 11, ga watan da muke ciki Fabrairu.

Kungiyar ta bayyana cewa karancin samarwa mambobin ta walwala a jami’ar ne dalilin shiga yajin aikin, wanda tace gwamnati ta gaza shawo kan matsalar.

:::Hukumar NDLEA ta kama dan shekara 75 mai siyar da kayan maye ga matasa

Shugaban kungiyar ASUU, reshen jamai’ar Kaduna Dr. Peter Adamu, ne ya sanar da hakan cikin wasikar da ya aikewa uwar kungiyar ASUU, ta kasa don samun damar shiga yajin aikin.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, ya rawaito cewa wasikar da shugabannin ASUU, reshen jami’ar Kaduna suka fitar tace gwamnatin jihar taki cewa uffan akan bukatun da suka gabatar mata.

Kungiyar ta kuma ce cikin abubuwan da take bukata akwai biyan malaman albashi na watanni 5, da kuma wani bashin da suke bin gwanati tun a shekarar 2017.

Bugu da kari sunce suna bin bashin alawus din kula da dalibai masu neman kwarewar aiki wanda ba’a biya ba daga shekarar 2021 zuwa 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here