A yau ne yan majalisa zasu dawo daga hutu da suka tafi

0
54

Yau ce ranar da ake kyautata zaton cewa mambobin majalisar wakilai zasu cigaba da zama bayan tafiya hutu a watan daya wuce.

A ranar 14 ga watan Junairu na 2025, ne majalisar tayi zama na farko a shekarar da muke ciki, sannan ta tafi hutu zuwa ranar 28 ga watan na Junairu don bawa kwamitocin ta damar kammala yin nazari akan kasafin kudin shekarar ta 2025.

Bayan hutun yau Talata, itace ranar da aka bayyana da cewa yan majalisar zasu cigaba da zama.

Akwai yiwuwar yan majalisar su tattauna kan batun dokar harajin Tinubu, da ta janyo cece-kuce.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here