Rusau din gwmanatin Kano ya kashe mutane 2 a Rimin Zakara

0
34

Rahotanni sun bayyana cewa akalla mutane 2, ne suka mutu sannan 4, suka jikkata sanadiyyar yin rusau a Unguwar Rimin Zakara, dake birnin Kano.

Mazauna yankin sun ce jami’an tsaro ne suka harbe mutane biyun da suka rasu yayin da ake aiwatar da rusau din karkashin jagorancin wakilan gwamnatin Kano.

Mutanen sun ce a daren jiya lahadi masu rusau din sun rushe gidaje fiye da 50, wanda hakan ya sanya mutane da yawa suka rasa muhallin su.

Wata Majiya tace anyi asarar dukiya mai tarin yawa, yayin da wasu fusatattun matasa suka zargi jami’an dake yin rusau din da karya umarnin kotu wajen aikata rusau.

Daga haka ne rikici ya kaure tsakanin yan unguwar ta Rimin Zakara, da jami’an rusau har hakan ya sanya jami’an tsaro yin harbin daya kashe mutane 2, da jikkata karin wasu 4.

Kawo yanzu dai ba’a ji martanin gwamnatin Kano akan wannan al’amari ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here