Rikicin masarauta yayi ajalin mutane masu yawa a jihar Osun

0
25

Rikicin ya samo asali bayan gwamnan jihar ya nada Prince Timileyin Oluyemi, a matsayin Olojudo na Ido Ayegunle a yankin Esa-Oke, dake karamar hukumar Obokon.

:::Masu gidajen mai sun fara siyan fetur daga matatun mai na Fatakwal da Warri

Al’ummar garin dai tun da farko sun bukaci gwamnati da ta daga darajar hakimin su a matsayin Olojudo na Ido Ayegunle maimakon nada musu sabon sarkin gargajiya.

Haka kuma, ‘yan asalin yankin sun yi ikirarin cewa yayin da Ido Ayegunle yake karkashin garin Esa-Oke, mutumin da gwamnatin jihar ta nada dan garin Ilesa ne.

Da yake tsokaci kan rikicin, wani basaraken garin Osolo na Esa-Oke, Adegboyega Ajiboye, ya ce wasu rufaffiyar fuska ne suka mamaye garin inda suka harbe mutane da dama.

Yace mutanen sun zo a cikin motocin bas guda 18 daban-daban kuma suka fara harbin mutane a Esa-Oke.

Jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sandan jihar Osun, Yemisi Opalola, ta ce rundunar ta san da faruwar lamarin, inda ta kara da cewa ana kokarin ganin an shawo kan lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here