Masu gidajen mai sun fara siyan fetur daga matatun mai na Fatakwal da Warri

0
32
man fetur
man fetur

Kungiyar masu siyar da albarkatun man fetur ta kasa PETROAN, tace mambobin ta sun fara yin lodin fetur daga matatun mai mallakin Nigeria, dake Fatakwal da Warri.

:::Rusau din gwmanatin Kano ya kashe mutane 2 a Rimin Zakara

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, mai magana da yawun PETROAN, Joseph Obele, ya ce lodin da aka fara ya kawar da shakkun cewa matatun man da ke karkashin kamfanin mai na Najeriya (NNPCL) basa yin aiki.

Obele, yace daga cikin kayayyakin da suka fara daukowa daga matatun Fatakwal da Warri, akwai Kalanzir, Gas, da kuma fetur.

A baya dai wasu daga cikin al’umma sun bayyana rashin amincewar su dangane da batun NNPCL, na cewa ya gyara matatun man Nigeria na Fatakwal da Warri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here