Kotu ta aike da Farfesa Usman Yusuf Gidan Gyaran Hali na Kuje

0
35

Wata babbar kotun tarayya dake birnin Abuja, ta bayar da umarnin tsare tsohon shugaban hukumar inshorar lafiya ta kasa Farfesa Usman Yusuf, a gidan gyaran hali na Kuje dake Abuja.

Mai shari’ah Chinyere Nwecheonwu, ce ta bayar da umarnin a yau Litinin bayan gabatar dashi a gaban kotun.

:::Gwamnatin Nigeria ta ja kunnen yan kasa akan barkewar cutar Ebola

Chinyere tace za’a cigaba da tsare farfesan har sai bayan kammala sauraron bukatar da aka kai mata ta bayar da shi beli.

Babbar kotun tarayyar ta dage cigaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 12 ga watan Fabrairu.

Idan za’a iya tunawa dai jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC, ne suka kama farfesan har gidansa dake Abuja, a makon daya wuce, bisa zargin sa da bayar da wata kwangila ba bisa ka’ida ba.

Shi dai Farfesa Usman Yusuf, yayi kaurin suna wajen sukar manufofin gwamnatin Tinubu, da wasu ke ganin cewa hakan na daga cikin dalilin kama shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here