Tsohon gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, yace babu wata mafita data zarce goyawa jam’iyyar su ta APC, baya a yanayin da Nigeria ke ciki.
Masari, ya sanar da hakan a jiya lahadi lokacin da yake yin jawabi a wajen kaddamar da yakin neman zaben kananun hukumomin jihar Katsina a karamar hukumar Kafur.
Gwamnatin jihar dai ta sanar da cewa za’a gudanar da zabukan kananun hukumomin a ranar 15, ga watan da muke ciki wato Fabrairu.
Masari, ya kuma kalubalanci masu shirin kafa wata jam’iyyar hadaka da manufar kifar da Gwamnatin Bola Tinubu, a kakar zabe mai zuwa, yana mai cewa rashin basu mukamin siyasa ne yasa suke yin wannan shiri.
Aminu Masari, ya kara da cewa ko da mutanen sun yi hadaka hakan bazai hana APC cigaba da rike mulkin Nigeria ba.
Masari ya ce a matsayinsa na wanda su suka kafa jam’iyyar APC, zai ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da manufofin ta da kuma ganin ta cigaba da samun nasara.