Gwamnatin tarayya ta karyata labarin da ke cewa tana yin shirye shiryen kara kudin wutar lantarki nan da wani lokaci kankani.
Mai bawa Shugaban Kasa shawara a harkokin makamashi Olu Arowolo, ce ta sanar da hakan cikin wata sanarwa da ta fitar tana mai cewa ba’a yiwa kalaman ta fahimta mai kyau ba, yayin da aka yada cewa za’a yi karin kudin wutar da kaso 65, cikin dari.
Kafafen yada labarai na kasar nan sun rawaito cewa Olu, tayi wannan kalamai a taron makamashi na Afirka da aka gudanar a birnin Dar es Salam na kasar Tanzaniya.
:::Rikicin masarauta yayi ajalin mutane masu yawa a jihar Osun
Sai dai tace manufar kalaman ta shine a bayan an ƙara kuɗin wutar na Band A a shekarar 2024, a yanzu kuɗin da ake samu daga wutar lantarkin ya na biyan kashi 65 ne cikin kuɗin da ake kashewa wurin samar da wutar, inda gwamnati ke cigaba da biyan giɓin da ake samu.
Ta kuma ce babban burin gwamnatin kasar nan shine ta inganta fannin samar da wutar lantarki da Kuma magance matsalar durƙushewar babban layin lantarkin.