Filin da aka yi rushe a Rimin Zakara mallakin Jami’ar Bayero ne—Gwamnatin Kano

0
45

Gwamnatin jihar Kano, ta mayar da martani akan dambarwar data faru ta rusau a unguwar Rimin Zakara, wanda rusau din ya zama sanadiyyar mutuwar mutane 2, da jikkata wasu da dama.

Gwamnatin tace filin da aka rushe mallakin jami’ar Bayero, ne da wasu suka siyar har al’umma suka gina gidaje a wajen.

:::Gwamnatin Nigeria ta musanta labarin karin kudin lantarki

Daraktan sashin hulda da jama’a na ma’aikatar filaye da tsare-tsare ta Kano, Umar Abdu, ne ya sanar da hakan a yammacin yau litinin.

Idan za’a iya tunawa dai a jiya lahadi cikin dare jami’an gwamnatin Kano, hadin gwuiwa da jami’an tsaro suka gudanar da yin rusau din gidajen da suka zarce 50, a unguwar ta Rimin Zakara.

Rusau, din ya haifar da tashin hankali sakamakon arangamar da aka samu tsakanin jami’an tsaron dake tare da masu rusau din da al’ummar da aka rushewa gidajen.

A lokacin an samu asarar rayukan mutane 2, da aka ce harsashin bindiga ya same su, sai wasu karin mutane 4, da suka jikkata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here